2 Yuni 2020 - 04:06
Kisan George Floyd : Zimbabwe Ta Kirayi Jakadan Amurka

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Zimbabwe, ta kirayi jakadan Amurka a kasar, domin bayyana masa bacin ran kasar a kan kisan bakar fatar nan George Floyd a hannun ‘yan sandan Amurka.

(ABNA24.com) Ma'aikatar harkokin wajen kasar Zimbabwe, ta kirayi jakadan Amurka a kasar, domin bayyana masa bacin ran kasar a kan kisan bakar fatar nan George Floyd a hannun ‘yan sandan Amurka.

Zimbabwe ta kirayi jakadan na Amurka ne a birnin Harare, bayan da Amurkar ta zayyano ta a cikin jerin kasashen da ta ce makiyanta ne daga cikin kasashen waje da ke rura wutar rikicin da ya barke a Amurka biyo bayan kisan na George Floyd.

A jiya Lahadi ne mashawarcin shugaban kasar ta Amurka kan harkokin tsaron cikin gida, Robert O’Brien, ya bayyana jin takaici game da kalaman da kasashen China, Rasha, Iran da kuma ita Zimbabwe, suka yi biyo bayan kisan na George Floyd.

Batun kisan bakar fatar George Floyd, da wani jami’in 'yan sanda mai suna Derek Chauvin ya yi a birnin Minneapolis, ya janyo tofin Allah-tsine da gagarumar zanga-zanga a Amurka, lamarin da ya sanya aka kafa dokar hana fita a birane da dama na kasar.




/129